Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 23:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Kun iya ba baƙo rance da ruwa, amma kada ku ba danginku rance da ruwa don Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan abin da za ku yi a ƙasar da kuke shiga, ku kuma mallake ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 23:20
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi.


Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa.


“Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”


Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.


za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”


Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba.


“Idan kun ranta wa jama'ata matalauta da suke tsakaninku kuɗi, ba za ku zama musu kamar masu ba da rance da ruwa ba. Kada ku nemi ruwan kuɗin daga gare su.


Kada ka ba shi rance da ruwa, amma ka ji tsoron Allah ka bar ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, ya zauna tare da kai.


Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa 'yan'uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.” Sa'an nan na kira babban taro saboda su.


Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.


Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.


wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama,


Zan husata, in sa a kashe ku cikin yaƙi, matanku, su ma, su zama gwauraye, 'ya'yanku kuwa su zama marayu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ