Dawuda ya ce masa, “Za ka yarda ka kai ni wurin maharan nan?” Sai ya ce wa Dawuda, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan nan suke.”
Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba, Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa. Ba daidai ba ne ka ba da waɗanda suka tsere a hannun maƙiyansu A ranar wahala.”
Kai mai tsarki ne, Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta. Kai da ba ka duban laifi. Me ya sa kake duban marasa imani? Kana iya shiru sa'ad da mugu yake haɗiye Mutumin da ya fi shi adalci?
Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.