Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 22:21 - Littafi Mai Tsarki

21 sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 22:21
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.’


'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.


Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila.


Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.”


Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”


to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.


'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.


sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


“Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila.


to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.


Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.


za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.


Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.


“Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.


Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya.


Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa.


Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.” Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”


ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.


“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ