“Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.
Ya kuma yi musu misali, ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. In ma an yi, ai, sai ya kece sabuwar tufar, sabon ƙyallen kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba.