M.Sh 21:5 - Littafi Mai Tsarki5 Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.
A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.