Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 21:15 - Littafi Mai Tsarki

15 “Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi 'ya'ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 In mutum yana da mata biyu, yana kuwa ƙaunar ɗaya, ba ya kuma ƙaunar ɗayan, su biyun kuwa suka haifi masa ’ya’ya maza, sai ya zamana cewa ɗan farin ya kasance na wadda ba ya ƙauna,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 21:15
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu.


Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.


Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”


to, a ranar da zai yi wa 'ya'yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin,


Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta haihuwa.


Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma'aka, ya zama shugaban 'yan'uwansa, gama nufinsa ya zama sarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ