Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 20:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya ci amfaninta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 20:6
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”


Za ki sāke dasa gonar inabi A kan duwatsun Samariya, Masu dashe za su dasa, Za su mori 'ya'yan.


Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?


“Sa'an nan shugabanni za su yi magana da jama'a, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda ya gina gidan da bai buɗe shi ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya yi bikin buɗewar.


Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ