Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 20:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, zai yaƙi magabtanku dominku, ya ba ku nasara.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 20:4
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”


Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”


Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku.


Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.


Ba mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku zai sa ƙasar ta firgita, ta ji tsoronku a duk inda kuka sa ƙafa, kamar yadda ya faɗa muku.


Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.


Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.


Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra'ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”


Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su?


Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”


Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.


Haka Ubangiji ya ceci Isra'ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.


Sa'ad da ka ji motsi kamar na tafiyar sojoji a bisa itatuwan tsamiya, sai ka fita ka yi yaƙi, gama Allah ya wuce ta gabanka don ya bugi sojojin Filistiyawa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ