Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 20:18 - Littafi Mai Tsarki

18 don kada su koya muku yin abubuwa masu banƙyama waɗanda suka yi wa gumakansu, har ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 20:18
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”


Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.


In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata.


Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu, Ku keɓe, in ji Ubangiji, Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki, Ni kuwa in yi na'am da ku,


Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”


to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


Kada kuma ku auro wa 'ya'yanku maza 'yan matansu 'ya'ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi'ar allolinsu, har su sa 'ya'yanku su bi allolinsu.


da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.


Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”


Duk wanda bai saurari maganata wadda zai faɗa da sunana ba, ni da kaina zan nemi hakkinta a gare shi.


Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai.


Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.


Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku,


“Sa'ad da kuka kewaye gari da yaƙi, kuka daɗe kuna yaƙi da shi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari har ku lalata su, gama za ku ci amfaninsu. Kada ku sassare su, gama itatuwan da yake cikin saura ba mutane ba ne, da za ku kewaye su da yaƙi.


Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.


Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al'ummai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ