Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 20:16 - Littafi Mai Tsarki

16 “Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 20:16
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.


sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.


Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.


A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.


Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.


Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.


Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.


Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.


Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.


Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al'umman da suke kusa da ku ba.


Za ku hallaka su ƙaƙaf, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa kamar yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku,


Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji.


A sa'ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.”


A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000).


Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.


Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.”


Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.


to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.


Ubangiji zai bashe su a gare ku. Za ku yi musu kamar yadda dā na umarce ku.


Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ