M.Sh 20:1 - Littafi Mai Tsarki1 “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”