“Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi, Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu. Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon, Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.
Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,