Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa.
“Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”
“Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.
Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda yake cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Gama Arnon shi ne kan iyakar Mowabawa da Amoriyawa.