16 Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani,
16 In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,
Kada ka bar ni a hannun magabtana, Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.
Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina, Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba.
Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,
Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.
Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.
“ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.