17 Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Abin da suka faɗa daidai ne.
17 Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau.
“Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama'an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne.
Zan tayar musu da wani annabi kamarka daga cikin 'yan'uwansu. Zan sa magana a bakinsa, zai faɗa musu duk abin da na umarce shi.
Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.
Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa, Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi. A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini.
Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi.
Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini, “Ga shi, na sa maganata a bakinka.