A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.
Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a'a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi.
Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”
Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.
“To fa, ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da sahihanci da aminci, ku yi watsi da gumakan da kakanninku suka bauta wa a hayin Kogin Yufiretis, da cikin Masar.