Wata rana muna tafiya wurin yin addu'a, sai muka gamu da wata yarinya mai aljani mai duba, tana kuwa samo wa iyayengijinta amfani mai yawa ta wurin dubar.
Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
Mutane za su riƙa ce muku ku nemi shawarar 'yan bori da masu sihiri waɗanda suke shaƙe muryar, har ba a jin abin da suke faɗa. Za su ce, “Ai, ma, ya kamata mutane su nemi shawara daga aljannu, su kuma nemi shawarar matattu saboda masu rai.”