Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 18:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra'ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 18:1
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin haka kabilar Lawi ba su da rabo ko gādo tare da 'yan'uwansu, Ubangiji shi ne gādonsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)


Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.


Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.


Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra'ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra'ilawa.”


Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra'ila, shi ne rabon gādonsu.


Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.


Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”


Lawiyawa kuma ba za su rasa firistocin da za su tsaya a gabana, suna miƙa hadayun ƙonawa ba, da hadayu na gari na ƙonawa, su kuma miƙa sadaka har abada.”


“Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra'ila ba, ni ne abin mallakarsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ