Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 17:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 17:8
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


“Ka tambayi firistoci a kan wannan doka.


Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’


Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.


sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.


Wannan shi ne tanadi domin wanda ya yi kisankai, wato wanda zai gudu zuwa can don ya tsira. Idan ya kashe abokinsa ba da niyya ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu a dā,


“Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi.


sai ku keɓe wa kanku biranen mafaka domin wanda ya yi kisankai da kuskure, ba da niyya ba, ya gudu zuwa can.


In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba,


“Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.


“Idan mutum biyu na faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.


“In mutum ya dūki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi.


Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.


Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.


In kuwa ba a sami ɓarawon ba, sai a kawo maigidan a gaban Allah don a tabbatar babu hannunsa a cikin dukiyar amininsa.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,


Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.


amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.


Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.


Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da take shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari'a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra'ila,


Kenaniya da 'ya'yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ