Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 16:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Ku kiyaye watan Abib don ku yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku, gama a watan Abib ne Ubangiji Allahnku ya fito da ku daga Masar da dad dare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ku kiyaye watan Abib, ku kuma yi shagalin Bikin Ƙetarewar Ubangiji Allahnku, domin a watan Abib ne ya fitar da ku daga Masar da dad dare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 16:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.


A wannan rana kuka fita, wato a watan Abib.


Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari.


Da maraice a rana ta goma sha huɗu ga watan fari, ita ce ranar Idin Ƙetarewa ta Ubangiji.


Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi.


To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa.


Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.


Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.


To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.


Sai ku miƙa hadayar ƙetarewa daga garkenku na tumaki da na shanu ga Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa.


A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra'ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.


Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ