“Domin haka, sai ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah ya ce, “Kuna cin nama da jininsa, kuna bautar gumaka, kuna kuma yin kisankai, da haka za ku mallaki ƙasar?
Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a.
Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.” Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.”
“Amma kwā iya yanka nama ku ci a garuruwanku duk lokacin da ranku yake so, bisa ga albarkar da Ubangiji yake sa muku. Mai tsarki da marar sarki za su ci abin da aka yanka kamar barewa da mariri.