Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 15:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Kowace shekara, kai da iyalinka za ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 15:20
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.


Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.


Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ