“Za mu kuma kawo hatsinmu na fari kullum, da sadakokinmu, da 'ya'yan itatuwanmu, da sabon ruwan inabi, da mai, a gaban firistoci, a shirayin Haikalin Allahnmu. “Za mu kuma ba Lawiyawa zakar amfanin gonakinmu, gama Lawiyawa ne suke tara zaka a garuruwanmu na karkara.
Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.
A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.
Ku kawo dukkan zaka a ɗakin ajiyata domin abinci ya samu a cikin Haikalina. Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.
Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir'auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na 'yan ƙanananku.”
Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir'auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir'auna ba.
Firist kuwa daga zuriyar Haruna zai kasance tare da Lawiyawa sa'ad da suke karɓar zakar. Lawiyawa kuma za su fid da zaka daga cikin zakar da aka tara musu, su kawo ɗakin ajiya na Haikalin Allah.