Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 14:21 - Littafi Mai Tsarki

21 “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 14:21
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”


“Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”


Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”


Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.


Duk wanda ya ci mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, ko shi Ba'isra'ile ne, ko baƙo ne, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, ya ƙazantu har maraice, sa'an nan zai tsarkaka.


Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”


Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”


Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.


sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.


za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa.”


Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.


Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.


Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.


Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”


Haka kuma za ku yi da 'ya'yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ