Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 14:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Gama ku keɓaɓɓun mutane ne na Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku kuwa ya zaɓo ku daga cikin dukan al'umman duniya ku zama mutanensa, wato abin gādonsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 14:2
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.


Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.


wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.


“Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa.


Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.


Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,” “Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!” Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,” “Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”


Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.


“Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


“Ya ɗan mutum, ka fuskanci Urushalima, ka yi magana gāba da masujadanta, ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila.


Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.” Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.


Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.


Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.


Hakika, yana ƙaunar jama'arsa, Dukan tsarkaka suna a ikonka, Suna biye da kai, Suna karɓar umarninka.


Gama sun auro wa kansu da 'ya'yansu 'yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”


Na kawo ka daga maƙurar duniya, Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa. Na ce maka, ‘Kai ne bawana.’ Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.


Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.”


Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai.


“Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ