Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 13:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi niyyar janye ku daga bin Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 13:10
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra'ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta.


Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.


Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”


Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.


“Namiji ko macen da yake da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”


ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.


“Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.’


Ya ce musu, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Kowane mutum ya rataya takobinsa, ya kai ya kawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango duka, kowa ya kashe ɗan'uwansa, kowa ya kashe zumunsa, kowa ya kashe maƙwabcinsa’ ”


to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.


Sai dukan jama'ar ƙasa suka tafi haikalin Ba'al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagaden. Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ