“Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.
Domin haka sa'ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”
har lokacin da Ubangiji ya zaunar da 'yan'uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa'an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’
Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.