M.Sh 12:21 - Littafi Mai Tsarki21 Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 In wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don yă sa Sunansa yana da nisa sosai daga inda kuke, za ku iya yankan dabbobi daga garkunanku na shanu da na tumakin da Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku, a cikin biranenku kuma za ku iya ci, yadda kuke so. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.