Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 12:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Amma sai ku ci su a inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Lawiyawa da suke a cikin garuruwanku. Sai ku yi murna a gaban Ubangiji Allah saboda duk abin da kuke yi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 12:18
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A nan, wato a gaban Ubangiji Allahnku, za ku ci, ku yi murna, ku da iyalanku, a kan dukan abin da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka da shi.


Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


Sa'an nan ya kawo su gidansa, ya kawo musu abinci, ya yi ta farin ciki matuƙa, domin shi da iyalinsa duka sun gaskata da Allah.


Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance,


Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.


Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka.


Amma adalai za su yi murna, Su kuma yi farin ciki a gaban Allah, Za su yi murna ƙwarai da gaske.


Dukanku adalai, ku yi murna, Ku yi farin ciki, Saboda abin da Ubangiji ya yi! Dukanku da kuke yi masa biyayya, Ku yi sowa ta farin ciki!


Ku da iyalanku za ku ci shi kowace shekara a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji zai zaɓa.


Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.


Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo.


Na gane iyakar abin da mutum zai yi, shi ne ya yi farin ciki, ya yi abin kirki tun yana da rai.


Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum.


amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ