Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 12:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Kada ku ci waɗannan a garuruwanku, zakar hatsinku, ko ta inabinku, ko ta manku, ko ta 'ya'yan fari na shanunku da tumakinku, ko hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, ko hadayarku ta ɗagawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 12:17
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ban ci kome daga cikin zakar sa'ad da nake baƙin ciki ba, ban kuma fitar da kome daga cikinta ba sa'ad da nake da ƙazanta, ban kuma miƙa wa matattu kome daga cikinta ba. Na yi biyayya da muryar Ubangiji Allahna, na aikata dukan abin da ka umarce ni.


A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.


“Sa'ad da kuka gama fitar da zakarku ta amfanin gona a shekara ta uku, wadda take shekara ta fid da zaka, sai ku ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu, don su ci, su ƙoshi a cikin garuruwanku.


Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.


sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.


Ku dubi ɗabi'ar Isra'ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba?


Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo.


Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ