A can ne za ku tafi, a can ne kuma za ku kai hadayunku na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi, da hadayunku na yardar rai, da 'ya'yan farin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki.
sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na wa'adi da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa.
amma sai a wurin nan ɗaya wanda Ubangiji zai zaɓa daga cikin kabilanku, nan za ku miƙa hadayunku na ƙonawa, nan ne kuma za ku yi dukan abin da na umarce ku.
Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”