M.Sh 12:10 - Littafi Mai Tsarki10 Amma sa'ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, sa'ad da kuma ya ba ku hutawa daga maƙiyanku waɗanda suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.