Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 12:1 - Littafi Mai Tsarki

1 “Waɗannan su ne dokoki da farillai da za ku lura ku aikata a ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku, ku mallaka dukan kwanakinku a duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗannan su ne ƙa’idodi da kuma dokokin da za ku lura, ku kuma kiyaye a ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku, yake ba ku don ku ci gādonta, muddin kuna zama a ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 12:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.


“Kamar kamen soja na tilas, Haka zaman 'yan adam take, Kamar zaman mai aikin bauta.


Zan yabe shi muddin raina. Zan raira waƙa ga Allahna dukan kwanakina.


Zan raira waƙa ga Ubangiji dukan raina, Zan raira yabbai ga Allah muddin raina.


Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.


su ne kalmomi, da dokoki, da farillai, waɗanda Musa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, bayan da sun fito Masar,


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


“Ga shi, na koya muku dokoki da farillai, yadda Ubangiji Allah ya umarce ni, don ku kiyaye su a ƙasa wadda kuke shiga ku mallake ta.


sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”


Na sa zuciya zan yi aminci, Game da kiyaye dokokinka!


Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai.


“A wancan lokaci ne na yi muku umarni, na ce, ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku wannan ƙasa, ku mallake ta. Dukan mayaƙanku za su haye da shirin yaƙi a gaban 'yan'uwanku, Isra'ilawa.


Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ