Ku tuna kuma da wahalar da kuka gani da idonku, da alamu, da mu'ujizai, da dantse mai iko mai ƙarfi wanda Ubangiji Allahnku ya fito da ku. Haka nan kuma Ubangiji Allahnku zai yi da dukan al'umman nan da kuke jin tsoronsu.
da abin da ya yi wa Datan, da Abiram, 'ya'yan Eliyab, ɗan Ra'ubainu, yadda ƙasa ta buɗe a tsakiyar Isra'ilawa ta haɗiye su da dukan 'ya'yansu, da alfarwansu, da dukan abu mai rai wanda yake tare da su.
Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra'ilawa.