da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi,
Kada ku ji tsoro, ku dabbobin saura, Gama wuraren kiwo a jeji sun yi kore shar. Itatuwa suna ta yin 'ya'ya, Itacen ɓaure da kurangar inabi suna ta yin 'ya'ya sosai.
Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”
Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko'ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”
Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.
Yanzu za ku ci abinci a wadace ku ƙoshi, Za ku yabi sunan Ubangiji Allahnku, Wanda ya yi muku abubuwa masu banmamaki, Ba kuma za a ƙara kunyatar da mutanena ba.