Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 11:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ƙasa ce kuma wadda Ubangiji Allahnku yake lura da ita, Ubangiji Allahnku yana dubanta kullum, tun daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 11:12
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan lura da su da kyau, in kuma komo da su a wannan ƙasa. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan kafa su, ba zan tumɓuke su ba.


Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu'arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.


Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa, Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.


Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,


Amma ikon Allah yana kan dattawan Yahudawa, saboda haka ba su hana su yin ginin ba, sai sun kai wa Dariyus labari, sun sami amsa a rubuce tukuna.


har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.


Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka! Inda ka tafi duka akwai wadata!


har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ