Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 10:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 10:22
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.


Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.


Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”


gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.


Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama, Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta, Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.


Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba.


Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar.


Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).


Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kamar yashi kuma dangam a bakin teku.


Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.


hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa.


Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne.


Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ