34 “Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce,
34 Da Ubangiji ya ji abin da kuka faɗa, sai ya husata, ya kuma yi rantsuwa ya ce,
Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,
Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi. Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”
Su wa kuma ya rantse wa, cewa ba za su shiga inuwarsa ba, in ba marasa biyayyar nan ba?
Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
Allah ya yi fushi sa'ad da ya ga haka, Don haka ya rabu da jama'arsa ɗungum.