Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.
Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”
Ai kuwa, an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai maganar da aka yi musu ba ta amfane su da kome ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba.