Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”
Ta ƙaƙa za mu hau? Gama 'yan'uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”
Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama'a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin 'yan'uwanku, da 'ya'yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”
“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.
Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.