Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”
Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”
Za su yi wa mutane shari'a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama'a tare da kai don ya yi maka sauƙi.