Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 7:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Gama ɗa yana raina mahaifi, 'Ya kuma tana tayar wa mahaifiyarta, Matar ɗa kuma tana gāba da surukarta, Mutanen gidan mutum su ne maƙiyansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 7:6
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da 'ya tata, 'yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”


'Dan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.


Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.


A cikinka ana raina mahaifi da mahaifiya, ana kuma tsananta wa baƙo, ana cin zalin marayu, da gwauruwa, wato wadda mijinta ya mutu.


Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’


Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.


Ko da iyayenku ma da 'yan'uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.


Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni.


Waɗanda kake amana da su, Za su kore ka daga ƙasarka. Mutanen da suke amana da kai, Za su yaudare ka, Su ci ka da yaƙi. Abokan nan naka da kake ci tare da su za su kafa maka tarko, Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayon nan nasa?’ ”


Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’


Gama har da 'yan'uwanka da gidan mahaifinka, Sun ci amanarka, Suna binka da kuka, Kada ka gaskata su, Ko da yake suna faɗa maka maganganu masu daɗi.”


Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.


Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.


Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi.


Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko'ina a ƙasar, yana hallakar da jama'a, kowa na ta kansa.


“Bari kowane mutum ya yi hankali da maƙwabcinsa, Kada kuma ya amince da kowane irin ɗan'uwa, Gama kowane ɗan'uwa munafuki ne, Kowane maƙwabci kuma mai kushe ne.


Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ