Mika 7:18 - Littafi Mai Tsarki18 Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.