A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.
Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.
Sa'an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”
Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.
Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, ‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.’ ”