Ya ku mutanen zamanin nan, ku saurari maganata. Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasar da take da kurama? Don me fa mutanena suke cewa, ‘Mu 'yantattu ne, Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.
Ya ku jama'ata, ku tuna Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla, Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya amsa masa, Da abin da ya faru daga Shittim, har zuwa Gilgal, Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”