Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 6:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba. Za ku matse 'ya'yan zaitun, amma ba za ku shafa mansa ba, Za ku kuma matse 'ya'yan inabi, amma ba za ku sha ruwansa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba; za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba, za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 6:15
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”


Kun matsa wa talakawa lamba, Kun ƙwace musu abincinsu. Saboda haka kyawawan gidajen nan da kun gina da dutse, Ba za ku zauna a cikinsu ba, Ba kuwa za ku sha ruwan inabin nan Daga kyawawan gonakin inabinku ba.


Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”


Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”


Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.


A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’


To, bari in shuka, wani ya ci amfanin, Bari a tumɓuke amfanin gonata.


Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, Ba kuma 'ya'ya a kurangar inabi, Zaitun kuma bai ba da amfani ba, Gonaki ba su ba da abinci ba, An kuma raba garken tumaki daga cikin garke, Ba kuma shanu a turaku,


to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.


Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra'ila, domin Isra'ilawa ko dabbobinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ