Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”
to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.
Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.”