Mika 6:12 - Littafi Mai Tsarki12 Attajiran birnin sun cika zalunci, Mazaunansa kuwa maƙaryata ne, Harshensu na yaudara ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!