Sai ma'auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.
Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce, Mu sami damar yin kasuwancinmu. Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne? Ko mā sami damar kai hatsinmu kasuwa, Mu sayar musu da tsada, Mu yi awo da ma'aunin zalunci, Mu daidaita ma'auni yadda za mu cuci mai saya?