Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba. Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala, Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya. Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.
Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.
Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!
Zan kuma hamɓare gadon sarautan daula, in kuma karya ƙarfin daular al'umman. Zan kuma hallaka karusai da mahayansu. Sojojin dawakai kuma za su kashe junansu da takuba.
Ubangiji ya ce, “Zan datse karusa daga Ifraimu, In datse ingarman yaƙi a Urushalima, Zan kuma karya bakan yaƙi. Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama, Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”